Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

00:00
00:00

Episode's summary

A wannan makon shirin ya yi leƙa yankin arewa maso gabashin Najeriya ne, inda ƙananan manoma ke kokawa kan yadda suka fama da tsadar takin zamani, makamashi na man fetur da dizal, a daidai lokacin da kuma hayar motocin noma na tantan ya gagari da dama daga cikinsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

Episodes

312-

Tsadar takin zamani da makamashi na barazana ga harkar noma a Najeriya

A wannan makon shirin ya yi leƙa yankin arewa maso gabashin Najeriya ne, inda ƙananan manoma ke kokawa kan yadda suka fama da tsadar takin zamani, makamashi na man fetur da dizal, a daidai lokacin da kuma hayar motocin noma na tantan ya gagari da dama daga cikinsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

15 Nov 2026
311-

Tsada da ƙarancin man fetur ya zame wa manoma ƙalubale a Maraɗi

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon ya leƙa jihar Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar inda noman rani ke cikin barazanar fuskantar koma baya, sakamakon ƙarancin man fetur da kuma tsadarsa, matsalar da ta tilasta wa wasu manoman dakatar da ayyukansu.

01 Nov 2026
310-

Najeriya ta karɓi baƙuncin taron Hukumomin Hasashen Yanayi na Duniya

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan taron Hukumomin Hasashen Yanayi na Duniya, wanda a karon farko ya gudana a nahiyar Afrika, kuma Najeriya ta karɓi baƙuncinsa a birnin Legas. Shirin ya kuma tattauna kan yadda har yanzu manoma da dama a Najeriya ke da shakku kan nau'ikan irin shuka da aka inganta. Sai a ,atsa alamar sautin da ke sama domin sauraron shirin.......

28 Oct 2026
309-

Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar tsuntsayen jan baki da ke lalata gona komai girmanta a duk lokacin da suka durfafeta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, wadda ta yi ƙamarin da har wasu manoma na cewa, dabarun da suka daɗe suna amfani da su wajen korar tsuntsayen sun kasa magance matsalar, lamarin da ya tilasta musu neman wasu sabbin hanyoyi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...........

03 Oct 2026
308-

Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar. A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar. Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.

26 Sep 2026